Kafofin yada labarai na Taiwan sun bayar da rahoton a ranar 6 ga Janairu, 2023 cewa sassan tattalin arzikin yankin Taiwan sun sanar da fadada takunkumin da aka kakaba wa Rasha da Belarus, wanda ya fara aiki nan take don hana kasashen biyu yin amfani da kayayyakin da ake samarwa a Taiwan don ayyukan soji.